Abin Al’ajabi: An haifi Saniya mai kai biyu a Yobe
1 - tsawon mintuna
Ikon Allah baya karewa, kuma dama dai ance idan Duniya tazo karshe za’ayi ta ganin sabani daban daban.
A jiya ne jaridar Rariya ta dauko hoton wata Saniya da aka haifa da kai biyu a garin Abuja, inda jaridar t daura hotunan Saniyar a shafinta na Facebook.
KU KARANTA:Abin Al'ajabi: Wani mutum mai yatsu 26
Jaridar tace an ga wannan abin mamaki ne a garin Nguru na jihar Yobe, inda aka haifi saniya mai kai guda biyu, daya a gaba, daya a baya, sai dai jaridar tace Jama’a sun tsorata da ita, hakan yasa suka kona ta.
Ku biyo labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng