Tashin hankali: Arewacin Najeriya, ya zamo gurin mutuwa – Sanata Sani

Tashin hankali: Arewacin Najeriya, ya zamo gurin mutuwa – Sanata Sani

-Sanata Shehu Sani yayi ma arewa lakkabi da gurin mutuwa

-Sani yace an jika yankin da jinin bayin Allah da dama

-Dan majalisan yayi Allah wadai da hare-haren bam da yan Boko Haram suka kai a kwanan nan

Dan majalisa mai kwalisa, kuma shugaban kungiyar masu agajin rikici a Arewa maso gabas, Sanata Shehu Sani, yayi Allah wadai da hare-haren bam da aka kai kwanan nan a jihar Borno da Adamawa.

Tashin hankalai: Arewacin Najeriya, ya zamo gurin mutuwa – Sanata Sani
Tashin hankalai: Arewacin Najeriya, ya zamo gurin mutuwa – Sanata Sani

A wata jawabi da dan majalisar ya yi a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, ya bukaci yan Najeriya da su amince da yihuwar kawo karshen ta’addanci.

Ya ce: “ta’addanncin addini shine tushen haram, yayinda talauci da rashin ci gaba yake gina shi. Dole Shugabannin siyasa da sarakunan arewa su farka ga wannan gaskiyar. Zaman lafiya da kuma ci gaba a arewacin Najeriya zai saura wani mafarki har sai mutanen yanking aba daya sun tashi a kan wadanda kin yin amfani, suke wulakanta addini don ci gaban siyasar su.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2017 zai kawo karshen koma bayan tattalin arziki - Buhari

“Indonesia da Malaysia su zamo abun kwaikwayo ga Arewa, amma ba wai Afghanistan ko Iraqi ba. Ta’addancin addini ya kasance wani gyambo me hadari ga Najeriya da yankunan ta.

“An shika kasar Arewa da jinin mutane bayin Allah tsawon shekaru da dama, da sunan rikicin addini. Lokaci yayi da kowa zai daga murya. Bindiga zai iya dakatar da bindiga na dan wani lokaci amma kakkausar murya zai iya dakatar da bindiga har abada.”

A cewar jaridar Punch, sanatan, wanda ke wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisa, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci yabo kan alkawarinsa, kafiya da kuma muhimmanci gurin dawo da doka, tsaro da kuma makamancin zaman lafiya a Arewa maso gabas.

Sani ya kuma yi kira ga “idon basira” yunkuri don magance rikici a Arewa maso gabas, cewa babu wani hanya da ya fi dacewa fiye da aiki a hada hannu tare da jiha da kuma kananan hukumomi, shugabannin gari da kuma kungiyoyin jama’a haka kuma da kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel