An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

– Anotonio Guterres ne sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

– Guterres zai maye gurbin Ban-ki Mon wanda wa’adin sa ke karewa

– Sabon Shugaban Zai hau kujera wata mai zuwa

An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya
An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta samu sabon Shugaba wanda zai maye gurbin Shugaba Ban-Ki Mon yayin da wa’adin sa ya cika. Ban-Ki Mon zai sauka daga kujerar ne Ranar farkon shekara mai zuwa.

Antonio Guterres tsohon Firayim Ministan Kasar Portugal ne na Kasar Turai, ya kuma rantse cewa idan ya hau zai yi gaskiya. Tsohon Firayim Ministan yayi alkawarin bin dokoki da muradun Majalisar Dinkin Duniya yayin da ya dare Shugabanci.

KU KARANTA: Sarkin Kano zai aurar da diya

An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya
An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Shekaran Jiya ne Jaridar Premium Times tace an gama shirin nada Ministar Kasar nan, Amina Mohammed a matsayin Mataimakiyar Shugabar Majalisar Dinkin Duniyan, kuma nan da wani dan lokaci za a sanar. Sai dao har yanzu ba a samu wani bayani ba. Fadar Shugaban Kasa dai tace ba ta san wannan maganar ba.

Sabon Sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniyan, Antonio Guterres yace zai kawo gyara a Majalisar. Antonio Guterres yace dole a ga canji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel