Abin Al'ajabi: Wani mutum mai yatsu 26

Abin Al'ajabi: Wani mutum mai yatsu 26

Wani matashi Omar Martinez mai shekaru 14 dake da yatsu 26 na fuskantar kalubalen ciyar da yan’uwansa tun bayan rasuwar iyayensa.

Abin Al'ajabii: Wani Mutum mai yatsu 26
Omar Martinez

Sai dai matashin Omar yace shi ya kan manta yanada yatsu 26 ma har sai yaga jama’a sun kura masa ido suna mamakin halittarsa.

KU KARANTA:An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure

Karin nauyi akan Omar shine tun bayan rasuwar iyayensa, shi ne ke daukan nauyin kanwarsa da sauran kannensa, Omar ya kanyi faskare da sauran ayyukan karfi don samar ma kanwarsa abinci.

Abin Al'ajabii: Wani Mutum mai yatsu 26
Yatsun hannaye 6

KU KARANTA:An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure

Omar tare da kannensa suna zaune a nahiyar Amurka ta tsakiya, kuma yana da yatsu 6 a hannayensa, sai yatsu 7 a kafafuwansa.

Abin Al'ajabii: Wani Mutum mai yatsu 26
Yatsun kafa 7

Sai dai Omar yace ya gaji wannan halitta ne daga kakan sa da mahaifinsa, wanda yace suma suna dauke da kwatankwacin wannan halittan.

Zaku iya bibiyan labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Ku kalli bidiyon Omar anan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel