Gwamnan Borno yayi wani muhimmin kashedi (Karanta)
- Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace idan ba'a magance matsalar talauci ba da samar da ingantacen ilimi ga al'umma ba za'a iya kawo karshen rigingimu irin na Boko Haram ba
- Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da kwamitin sa ido akan yadda ake raba kudaden da aka kebewa 'yan gudun hijira a karkashin jagorancin Sanata Shehu Sani ya ziyarceshi a fadarsa dake Maiduguri
Kwamitin na binciken yadda aka yi anfani da kudaden 'yan gudun hijira ne a jihohin da rikicin Boko Haram ya daidaita inda kuma ake da dimbin 'yan gudun hijira da basu koma muhallansu ba.
Gwamnan yace sun shiga matsaloli da yawa cikin shekaru biyar zuwa shida da suka gabata amma yanzu an soma samun sauki.
KU KARANTA: Dalilin da yasa muke boyewa jama'a bayan mun lashe zabe inji kakakin majalisar Katsina
Gwamnan yace idan ba an magance matsaloli irin matsanancin talauci da ya addabi al'umma ba da kuma bunkasa harkokin ilimi, musamman ga marasa galihu "ina tsoron cewa rikicin Boko Haram ba'a ga komi ba yanzu bisa ga abubuwan da zasu faru nan gaba", inji Shettima.
Gwamnan ya ambato kidigdigan da bankin duniya ya fitar. Alkalumma sun nuna akwai dangantaka tsakanin talauci da irin rigingimun dake faruwa kamar na Boko Haram. Gwamna Shettima yace rahoton bankin duniya ya sake jaddada cewa shiyar arewa maso gabashin Najeriya da Chadi da Kamaru da yankin Dafur dake kasar Sudan da Nijar su ne yankunan da suka fi kowa talauci a duk fadin duniya.
Inji gwamnan, kashi casa'in cikin dari na 'yan gudun hijira daga jihar Borno suke. Wadanda suke jihar Adamawa duk 'yan Borno ne. Amma saboda abun da za'a samu jihohi da dama kan ce suna da 'yan gudun hijira amma abun ba haka ba ne.
Yace sansanin 'yan gudun hijira da aka ce yana Abuja ba na 'yan jihar Borno ba ne. Sansani ne na wadanda suke fama da kuncin rayuwa suka kai kansu can. Gwamnan yace abun takaici shi ne mutane na fakewa da abun dake faruwa a jihar Borno su azurtar da kansu. Ko a jihar Borno akwai kungiyoyi masu zaman kansu fiye da dari biyu amma ba'a ganin irin tallafin da suke ikirarin bayarwa. Yace har ma sun sa otel otel da gidajen haya sun yi tsada saboda yadda suke kwararowa zuwa Bornon.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng