Kalli hoton auren dan Civil Defence
1 - tsawon mintuna
LHotunan auren Wani ma'aikacin civil defence sun sosa zukatan ma'abota amfani da dandalin sadarwa.
Wani mutum mai suna Ubong Essien ma'aikacon civil defence ne da matar sa Inemesit Essien, sunyi hotunan su na kafin daura aure masu burgewa.
Ma'auratan yaren Ibibio ne, kuma sun tsara zasuyi auren su a Akwa Ibom.
An yarda za'a daura auren ranar asabar 10 ga watan Disamba shekarar nan, a garin Uyo, jahar Akwa Ibom.
Gaba dayan su sunyi kyau, sun kayatar, kuma alamu sun nuna amaryar tana farin cikin samun kyakkyawan mijin ta.
Da fatar samun zama lafiya ga ma'auratan.
Ku biyo mu a shafin mu na tuita@naijcomhausa.
Asali: Legit.ng