An yanke wa barawon kifin ruwa wata 4 a gidan yari
Wani babban kotu a Evbouriaria a babban birnin Benin, jihar Edo ta yanke ma wani matashi mai shekaru 22 Sylvester Livinus daurin watanni hudu a gidan yari saboda ya saci kifin ruwa guda 10.
Hukumar News Agency of Nigeria sun ruwaito cewa babban Alkalin kotun C.E. Oghuma ya kuma ba wanda aka dauren damar biyan naira 5,000 a matsayin kudin tara.
Da farko, mai hukuncin, Olatoye Oluwaseun, ya bayyanawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Satumba, da misalign karfe 2:45 na ranar a gida mai lamba 1, unguwar Toronto Benin.
KU KARANTA KUMA: Sojin ruwan Najeriya sun lalata matattun mai na bogi
Oluwaseun yace kifin ruwan mallakar Noma Okunbor ne kuma farashin su ya kai naira 10,000.
Yace laifin ya sabawa sashi 309 (9) na laifi.
Asali: Legit.ng