Abunda muka sani kan Auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi

Abunda muka sani kan Auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi

Labarai game da auren Zahra Buhari, daya daga cikin yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari da kyakkyawan dan biloniya ya samu cece kuce a jaridun Najeriya da shafukan zumunta nay an wasu makonni.

An tattare bikin auren, ranar auren, gurin auren, da yawan manyan baki da zasu halarci taron taya masoyan biyu murna cikin mamaki.

Abunda muka sani kan Auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi
Ahmed Indimi da Zahra Buhari

Hukumar Legit.ng ta lissafo wasu gaskiya tare da bayanin abunda muka sani da kuma abunda bamu sani ba game da auren shekaran.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya zama keke napep a Lagas

1. Zahra Buhari na shirin auren Ahmed Indimin ta, dan biloniya Mohammed Indimi a babban masallacin Abuja a ranar Juma’a, 2 ga watan Disamba 2016.

2. An kawo rahotanni, game da shugaban kasa Buhari kan halayensa da tsarin rayuwarsa, inda ya bukaci auran ya kasance cikin sauki, kuma makusanta da abokan arziki ne kawai zasu halarta.

3. Ahmed Indimi ya hadu da shugaban kasa a fadar shugaban kasa, a ranar 21 ga watan Nuwamba, inda suka tattauna cikin sirri bayan kafofin labarai daban-daban sun rubuta cewa hankalin shugaban kasar bai gama kwantawa da zabin yar tasa ba.

4. An rahoto cewa Ms Buhari da Mista Indimi sun hadu da juna kimanin wata daya da ya wuce- wannan ya sa abun ya damu shugaban kasa Buhari a matsayinsa na uba mai kula.

5. Dan bincike kadan a rayuwar angon ya nuna cewa shi kan shi ya kusa zama biloniya, yana da tarin ilimi, da kuma mutunci. Ba tare da dogon zance ba- Zahara da Ahmed sun dace da juna.

6. Daga baya, an kawo wani bayani game da cewa an daga auren zuwa ranar 9 ga watan Disamba, wannan yasa kowa ke mamaki ko akwai matsala ne.

A halin yanzu wasu majiya sun bayyana cewa an daga auren ne saboda Buhari bazai samu halartan bikin ba saboda wani taron mai muhimmanci ga Najeriya sai dai idan an canja ranar.

KU KARANTA KUMA: Yar wasa Chika Ike ta fito sanye da rigar naira miliyan 2

7. Kwanan nan Zahra ta amshi kyautar ban girma daga gidan Indimi- jakunkunan lefe na LV cike da diamond, sarkokin gwal, takalma masu kyau, jakunkunan rataya wa, super wax, leshi, turaruruka, kayan kwalliya da sauransu.

8. A halin yanzu, mugayen harsuna na ci gaba da cewa shugan kasa bai yarda da auren ba, da alama gidan Indimi na dokin kasancewar Zahra daya da cikin ahlin su- surukar Zahra Buhari ta yada wani rubutu, inda ta yabe ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel