Maigadi ya saci kayan da yake gadi (HOTUNA)
Wani Maigadi ya ci dukan tsiya a hannun jama’a tare da dauri bayan an kama shi ya fasa shagon da aka ba shi gadi inda ya saci burodi.
Maigadin mai suna Peter Langat Kipkirui ya fasa shagon Ubangidansa ne a unguwar Syokimau na garin Machakos, kasar Kenya.
Jama’an yankin sun yi ma Peter duka, tare da daure shi a jikin Falwaya bayan ya saci burodin daga shagon Gateway Mall inda yake gadi, dama dai masu siyar da burodi a yankin sun dade suna korafi kan yadda ake sace musu burodi a shagunan su, toh ashe barawon na gida ne.
KU KARANTA: Ƙaramin yaro ya ƙera fitila mai amfani da hasken rana
Ubangidan nasa ne ya hada mai tarkon data kama shi, inda ya sanya kwandon burodi da dama wani waje na musamman,don yaga wanda zai zo ya sace su, yayin da suke labe suna dakun suga wanene barawon, sai ga Peter yazo zai sace su, nan fa sukayi caraf da shi, inda basu yi wata wata ba suka hau shi da duka, daga karshe suka daure shi jikin Falwaya.
Asali: Legit.ng