Buhari, da matarsa sunyi bikin zagayowar haihuwar jikarsu

Buhari, da matarsa sunyi bikin zagayowar haihuwar jikarsu

A ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba, daya daga cikin jikokin shugaban kasa Muhammadu Buhari da matarsa, Zee ta kara shekara kuma kakkaninta sunyi mata bikin zagayowar haihuwar tata a Aso Villa.

Buhari, da matarsa sunyi bikin zagayowar haihuwar jikarsu
Aisha Buhari, mijinta da kuma uwar gayyar taron

A gurin bikin cikar jikar tasu shekaru 4 a duniya, anga shugaban kasa da matarsa, Aisha Buhari suna daukar hoto tare da jikar tasu, yayinda suka taimaka gurin yanka kek din da akayi mata na musamman. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya farin rigar yadi da wando da kuma hula yayinda Aisha Buhari ta sanya dinkin riga da siketi na atampa, dankwali da kuma mayafi.

KU KARANTA KUMA: Yar wasa Chika Ike ta fito sanye da rigar naira miliyan 2

Bayan cewa kakkanin nata sunyi kyau sosai, anga ita uwar gayyar sanye da doguwar riga yar kanti ja da afarari yayinda da ta tsaya a gaban kakkan nata don yanka kek din da akayi mata musamman domin wannan rana ta haihuwarta.

Barka da zagayowar shekara!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng