Garin neman ƙiba, budurwa ta samo rama
1 - tsawon mintuna
Hausawa na cewa garin neman ƙiba ake samo rama, hakan ta kasance da wata budurwa da tayi kokarin kara ma mazaunanta girma ta hanyar yin amfani da allura.
Wata budurwa ma’abociyar kafar sadarwa ta facebook Emmanuel Chinedu Udoaku ce ta bada labarin wata kawarta da ta aikata wannan aika aika, inda ta janyo ma kanta jangwam.
KU KARANTA: Abin ban dariya:Obasanjo ya koma alkalancin Ƙwallo
Udoaku ta roki jama’a dasu sanya kawarta cikin addu’a sakamakon halin da samu kanta bayan alluran da tayi na karin girman mazaunin ya kumbura mata cinya.
Jama’a wannan abu da mai yayi kama?
Za'a iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng