Wani ‘dan fashi ya bayyana sirrin aikin su

Wani ‘dan fashi ya bayyana sirrin aikin su

- Wata mata ‘yar fashi ta tona yadda suke aikin na su

- ‘Yan sanda sun kama masu fashi bisa hanya

- Wadannan ‘yan fashi sun yi kaurin suna Abuja da Kano

Wani ‘dan fashi ya bayyana sirrin aikin su

 

 

 

 

Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wasu manyan barayi 'yan fashi har guda 8 a Yankin Abuja/Kogi/Kano. Cikin wadanda aka kama akwai wata ana ce mata Hajiya, Hajiya Rekia Musa tayi karatu a Jami’ar Jihar Kogi, kuma ta rabu da mijinta kwanaki.

Hajiya Rekia tace ta kasance mai aiki tare da ‘yan fashin a matsayin mai samu labaran kus-kus tun watanni hudu da suka wuce. Yanzu haka dai ‘Yan Sanda sun kama tawagar wannan ‘Yan fashi.

KU KARANTA: An kori Koci ana cikin wasa

Jaridar Punch ta rahoto cewa kwanaki wadannan ‘yan fashi sun tare wasu ‘Yan Siyasa, inda suka saci Miliyan 200. ‘Yan fashin dai sun ce ba su sata idan ba wajen barawon dan siyasa ba, wanda shi ma ya sato kudin ne

A wata Kasa kuwa, Wani matashi ya nemi Kotu ta cigaba da tsare mahaifin sa har sai illa-Masha Allahu. Wannan matashin yace mahaifin na sa ya saka masa cutar kanjamau tun yana jariri don haka yake nema a Hukunta uban sa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng