Shekarar su 10 suna soyayya, yanzu za su yi aure
- Ola Moses zai auri Temi bayan sun kwashe shekara-da-shekaru suna soyayya
- Shekarar tsunstayen goma suna soyewar su

Kamar dai yadda Hausawa kan ce: Abu karamar wasa, karamar magana ta zama babba…Wadanna bayin Allah sun shafe shekaru fiye da goma suna tare, ga shi Allah yayi za su kuma yi aure.
Kamar yadda Sahibar ta fada, Temi tace tun shekarar 2006 suka hadu a Coci wajen bauta, Moses ya kuwa tambaye ta lambar waya, nan take ta mika masa. A wancan lokaci ana yayin waya kyauta da tsakar dare… Shekaru goma kenan, ga shi yau, za suyi aure.
KU KARANTA: Ashe tusa na magani?
Timi tace kafin sa, ba ta taba soyayya a duniya ba, kuma shine na karshe. Timi tace Moses ya nuna mata yadda ake soyayya a rayuwa, kuma da shi kadai ta taba yi. Timi tace lokacin da Ola Moses ya tafi Kano, ta zaci ba zai dawo ba.
Suka ce an ta kokarin a ga bayan su a rayuwa, sai dai Ubangiji ya kaddara za su auri juna. Tace har jina-jina iyayen ta sun taba yi mata, amma ya zama Tarihi.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng