Wacece matar sabon Gwamnan Jihar Ondo?
- Ko ka san Uwargidar Gwamna mai jiran gado, Misis Akerodolu
- An kammala zaben Jihar Ondo, inda dan takarar APC yayi nasara da kuma Rotimi Akerodolu ne ya lashe zaben
![Wacece matar sabon Gwamnan Jihar Ondo? Wacece matar sabon Gwamnan Jihar Ondo?](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt2effqi0har6.jpeg?v=1)
Ko shin wacece Misis Akeredolu? Mai dakin sabon gwamnan jihar Ondo, mai jiran gado? Mun kawo maku abubuwa 5 da ba ku sani ba game da Ran ta ya dade, Misis Betty Akeredolu:
Matar Sabon Gwamnan Jihar Ondo, mai jiran gado mutumiyar kasar Inyamurai ce. Nee Anyawu ta fito daga Emeabiam, Owerri a jihar Imo.
Misis Betty Akeredolu tayi fama da cutar cancer na mama a baya. Tuni yanzu ta murmure, har ta bude Kungiya mai kula da irin wannan cuta.
KU KARANTA: Akeredolu ya lashe zaben Jihar Ondo
Matar Gwamnan mai jiran gado a Jihar Ondo tana da digiri har biyu a kan fannin noman dabbobi. Tayi karatun kiwon kifi a Kasar Philippines, tana kuma da gona a Ibadan.
Misis Betty tana shekaru fiye da 60 a duniya, kuma tana da ‘ya ‘biyar, ciki guda na da aure, don haka tana da jika.
![Wacece matar sabon Gwamnan Jihar Ondo? Wacece matar sabon Gwamnan Jihar Ondo?](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkytknk0mco6ork.jpeg?v=1)
Kullum tana bayan Mijin ta, ko a wajen yakin neman zaben nan, da ita aka yi tafiyar tun shekaru hudu da suka wuce.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng