Yau ne ake gudanar da zaben jihar Ondo

Yau ne ake gudanar da zaben jihar Ondo

- Yau ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar.

- Hukumar zaben Nigeria INEC tace ta shirya tsaf dan tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihar.

- Haka kuma an tanadi dukkan kayan aiki da ake bukata dan gudanar da wannan aiki.

Yau ne ake gudanar da zaben jihar Ondo

Jam'iyyu 28 ne dai za su fafata kuma hukumar zaben kasar ta ce ta kammala dukkan shirye shirye na gudanar da zaben.

Kuma zaben na jihar Ondo ya dade ya na daukar hankalin al'umar kasar, ganin irin barakar da ta kunnu kai tun wajen tsaida 'yan takara a manyan jam'iyyun siyasar kasar wato jam'iyya APC mai mulkin kasar da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

KU KARANTA: Obasanjo ne kakan cin hanci da rashawa a Najeriya - Majalisar Wakilai

A wani labarin kuma, Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta ce zata tura jami’anta 26,000, jirage masu saukar Ungulu 3, motocin Sulke 12, da kuma kananan jiragen ruwa na tsaro, zuwa jihar Ondo, domin tabbatar da kwanciyar hankali, yayin gudanar da zaben Gwamna.

Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya sanar da haka yayin wani taro tsakaninsa da Jami’an hukumar shirya zaben kasar INEC, da kuma Jam’iyyun Siyasa.

Sifeto Janar Idris, ya ce za’a tura jami’an ‘yan sanda 5 zuwa kowane akwatin zabe da ke jihar, yayin gudanar da zabe. Sifeto Janar din ya kuma kara da cewa kananan jiragen tsaro 20 za’a tura zuwa yankunan da suka yi iyaka da ruwa, domin dakile yunkurin ‘yan ta’addan yankin Niger Delta na tada zaune tsaye.

A jiya Talata ne dai 22 ga watan Nuwamba, jam’iyyun Siyasa 16 a Najeriya, suka bukaci a dage zaben Gwamna a jihar ta Ondo da ke kudancin kasar, da za a yi a ranar 26 ga watan Nuwamba.

Kiran gamayyar jam’iyyun adawar na zuwa kwanaki kadan bayan da babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta bukaci da a dage zaben saboda dalilan tsaro.

Cikin wata takardar bayan taro da suka rattabawa hannu, Jam’iyyun adawar sun ce kiran ya zama tilas, saboda kaucewa aukuwar kazamin rikicin siyasa a jihar ta Ondo, idan har aka gudanar da zaben na Gwamna kamar yadda aka tsara.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: