Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

Dan majalisar wakilai da aka dakatar Abdulmumin Jibrin da matarsa Maryan Augie sunyi bikin murnar zagayowar aurensu a yau, 24 ga watan Nuwamba.

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

Jibrin ya je shafinsa na Instagram don ya nuna wa kyakyawar matar tasa irin so da kulawa da yake yi mata. Abu na farko da ya buga ya kasance hoton ta tana murmushi sannan ya ce: “Da Maryam a gefenka, je ka kwanta kawai!!! Yaro, je ka kwanta… Da irin wannan murmushi na dun-dun-dun a fuskarta sa’oi 24, sannan kuma ana tambayana dalilin da yasa nake tsalle a ko da yaushe kamar karamin yaro? Na kasance mijin Hajiya mai aji.”

KU KARANTA KUMA: Ma’aurata sun tarbi tagwaye bayan shekaru 20 da aure

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

Ya buga hotunan fuskarta ya kuma bayyana cewa 24 ga watan Nuwamba ya kasance ranar haihuwarta kuma. Yace: “Masoyiyata, duk ranar 24 ga watan Nuwamba na kasance wa ranar murna biyu ga ke da mu- ranar haihuwarki kuma ranar zagayowar aurenmu."

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

 “Murnar ranar haihuwa ga wannan baiwa mai son zaman lafiya da tausayi, abokiya mai biyayya, ya mai tarbiya, kanwa mai kula, sirika wacce ta cancanta, uwa ta gari kuma matar alfahari gare ni, Maryam Augie-Jibrin.”

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

 “Allah Ubangiji ya ci gaba da baki nisan kwana cikin koshin lafiya, zaman lafiya, nutsuwa da ci gaba… Allah ya saka ma kokarinki mara karewa, sadaukarwa.”

KU KARANTA KUMA: Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2017 mako mai zuwa

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

Ya karkare tsarin soyayyarsa ta hanyar buga wani hoton tare. Ya rubuta a hoton: “Murnar zagayowar ranar aure!!! Da wuya a yarda amma da wuya wata rana ta wuce ba tare da munyi dariya ba.”

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

 “kamar yadda na fada a lokacin aurenmu, ina ji ajikina nine namiji mafi wayo a duniya da na ciri tuta a kankisannan kuma aurenki na daya daga cikin shawara mafi kyau da na taba daukar ma kaina. Ina jin haka yanzu fiye da da.

Hotunan Abdulmumin Jubrin da kyakyawar matarsa

 “Abunda zan iya cewa shine Masha Allah… Allah ya karo albarkansa a kanmu ya kuma kare mu daga baki da idanun mugayen mutane.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: