Dan wasan Barcelona, Neymar za shi gidan yari
- Shegen dan wasan nan na Kungiyar Barcelona zai iya shiga gidan yari
- Neymar ya shiga matsala game da cinikin sa zuwa Barcelona shkearu 3 da suka wuce
- Dan wasan na Brazil, Neymar Jr. na iya kwashe shekaru biyu a Gidan maza
Hatsabibin matashin Dan wasan nan na Kasar Brazil, Neymar Jr ya shiga cikin babbar matsala a halin yanzu. Dan wasan na iya zarcewa kurkuku idan ba ayi wasa ba. Hukumar Kasar Spain suna kira da a daure Dan wasan inji BBC.
Akwai hannun Dan wasan a wata badakala cikin cinikin sayan sa da aka yi daga Kungiyar Santos zuwa Kungiyar Brazil shekarun baya kadan da suka wuce. Ana dai zargin dan wasa Neymar Jr. da Mahaifin sa da laifi.
KU KARANTA: An janye yajin-aiki?
Alkalin shari’ar, Jose Perals ya jaddada cewa dole a kama Tsohon Shugaban Kungiyar ta Barcelona, Sandro Rosell. Mista Rosell ne dai ya sayo Dan wasan daga Kungiyar Santos zuwa Barcelona a shekarar 2013.
Shekaru biyu da suka wuce ne dai dole ta sa Sandro Rosell ya sauka daga matsayin na sa saboda laifin da aka kama sa da shi. Ana zargin rashin gaskiya wajen cinikin dan wasan Neymar da aka saya kusan Miliyan €60.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng