Ba ruwan jam'iyyar mu da rikicin ku, APC ta cewa PDP

Ba ruwan jam'iyyar mu da rikicin ku, APC ta cewa PDP

- Sakataren jam'iyyar APC na kasa Mai Mala Buni ya musanta zargin cewar jam'iyyarsu ce take haddasa rikicin dake wakana a jihar Ondo, jihar da zata yi zaben gwamnanta mako mai zuwa

- A wata fira da yayi da majiyar mu, sakataren jam'iyyar APC na kasa Mai Mala Buni yayi tsokaci akan korafe korafen da mutane keyi dangane da zaben da za'a gudanar a jihar Ondo

Ba ruwan jam'iyyar mu da rikicin ku, APC ta cewa PDP

Injishi duk wanda ya san yadda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ke gudanar da mulki, ya san baya sa baki a harkokin zabe. Ya na son kuri'ar kowa tayi tasiri a zabe. Baya bukatar a sa baki a harkar kowace jam'iyya.

Mai Mala Buni yace abun dake faruwa a Ondo yana faruwa ne tsakanin jam'iyyar PDP wadda ta raba kanta da kanta, ta haifar da bangarori biyu, na Makarfi da Modu Sheriff. Babu ruwan jam'iyyarsu, injishi.

KU KARANTA: Abdulmumin Jibrin zai nemi takarar shugaban kasa a 2019

Akan damar da kotun koli ta baiwa wani dan takarar PDP yaci gaba da daukaka kara a kotun daukaka kara yace su basu damu da wannan ba saboda duka abun dake kawo cikas kin bin kaida ne. Yace yayi imani hukumar zabe ka'ida take bi kuma babu abun da zai hanata aikata gaskiya.

Mai Mala Buni yace su ashirye suke su yi zabe kuma basu ga abun da zai kawo tsaiko ba.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng