Hoton wani mutum da macizai
Wani bidiyo mai tsoratarwa na wani mai kama maciji a kasar India wanda ya saki wani katon buhu da macizai fiye da 200 , kamar kumarci da sauran su a daji.
Kamar yadda rohoto yazo , an tabbatar da cewa ya fidda macizai akalla 285 a cikin dajin,kuma anyi rohoton cewa sai da suka tabbatar da cewa ba wani kusa kafin su saki macizan.
An dauki bidiyon a dajin Panchmandi a yankin Hoshangabad.
KU KARANTA:
Salem Khan mutumin da saki macizan yace" mun saki macizai kamar 285 a cikin tsakiyar daji bayan su tabbatar da cewa ba wani mahaluki da ke kusa.
Ya kamata mu ceci macizai saboda abokan mu ne, ba makiyan mu ba , kuma manyan abokan manoma ne saboda suna kashe mana beraye a gona ki.
Khan wanda aka fi sani da Salem mutumin maciji, ana rohoton cewa suna sakin macizai 100- 200 a ko wanne wata.
Asali: Legit.ng