Dalilai 4 da suka sa Zahra Buhari ta dace da Ahmed Indimi

Dalilai 4 da suka sa Zahra Buhari ta dace da Ahmed Indimi

A ko da yaushe Kudi da mulki suna dacewa da juna. Zahra Buhari na daya daga cikin ‘ya’yan da ko wani mutumin Najeriya zai zo ya kasance da. Ta kasance mai kirki, hali mai kyau kuma mace ce mai himma sosai. Ahmed Indimi ya kasance dan biloniya mai harkan mai, Mohammed Indimi dan Maiduguri. Masoyan zasu kasance ma’aurata nan da dan makonni kalilan.

Aure abune mai kyau da ni’ima. Idan masoya masu tasowa guda biyu suka hadu suka kuma yanke shawarar kasancewa tare har iya rayuwarsu, lokacin ne na murna da farin ciki ga kowa. Zahra da Ahmed sun dace kuma bazamu taba gajiya da yayan masu kudi da mulkin guda biyu ba.

KU KARANTA KUMA: Tattalin arziki ya kara samun nakasu

Ga dalilin da yasa suka dace da juna

1. Dukkansu biyu na da kyau

Dalilai 4 da suka sa Zahra Buhari ta dace da Ahmed Indimi

Zuwa yanzu dukkan yan Najeriya sun san cewa Zahra Buhari na da kyau kuma mijin da zata aura Ahmed Indimi ya kasance mai kwarjini. Zamu iya fada maku yayansu zasuyi gadon tsan-tsar kyau.

2. Kudi da mulki

Dalilai 4 da suka sa Zahra Buhari ta dace da Ahmed Indimi

Zahra Buhari ta kasance yar Fulani matashiya wacce ta kasance yar shugaban kasar Najeriya mai ci a yanzu, shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ahmed Indimi ya kasance dan biloniya, Mohammed Indimi. Ya kuma kasance manajan talla na kungiyar Oriental energyresources. Idan kayi maganar kudi da mulki, babbu shakka wadannan masoya kenan.

3. Karancin shekaru ga kuma ilimi

Dalilai 4 da suka sa Zahra Buhari ta dace da Ahmed Indimi

Zahra ta kammala karatunta na digiri a kan ilimin hallita (micro biology) daga jami’ar Surrey. Matashiyar ta kasance mai jakadar SCAF mai himma, kungiyar da aka gina don rage rikicin sikila a fadin kasar. Ahmed ya kammala digirinsa a jami’ar prestigious ya kuma kasance matashi mai himmar aiki wanda ya cancanci daraja kamar mahaifinsa biloniya.

4. Yan arewa, musulmai kuma masu alfahari

Dalilai 4 da suka sa Zahra Buhari ta dace da Ahmed Indimi

Ahmed Indimi ya fito daga Maiduguri. Wata jiha a yankin arewacin Najeriya. Zahra ta kasance yar Fulani wacce aka rena a kan tafarkin musulunci. Ta kasance mai alfahari da al’adarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng