Wata budurwa ta saka kayan aure a ranar auren saurayin ta

Wata budurwa ta saka kayan aure a ranar auren saurayin ta

- Wata amaryar a Ghana an bar ta cike da mamaki , saboda budurwar mijin ta ta shigo ranar bikin su                                 

- Budurwar ta saka kayan aure, kuma tazo gurin bikin dan ta tona boyayyar alakar su da angon, kuma tayi kokarin dawowa da mijin gare ta                                                                  

- Duka abun an dauke shi a kamara kuma a yayin da akabar yan bikin cike da mamaki

Wata budurwa ta saka kayan aure a ranar auren saurayin ta

An tozarta wata amarya a Ghana kuma an barta cikin rudani a ranar auren ta, a lokacin da suka furta alkawulla da ita da mijin ta a lokacin addu'ar auren , wata yarinya ta shigo gurin bikin da kayan aure a jikin ta.

An bayyana yarinyar da ta shigo a matsayin budurwar angon da suke mu'amala a boye, wanda ya hargitsa amaryar.

Yarinyar ta dauki bututun magana, inda ta bayyana a yaren su cewa ita budurwar mijin ce ta boye, mutane sun ja baya dan mamaki, amma sai suka yi kokarin hanata tarwatsa bikin.

KU KARANTA:

Amaryar tayi kokarin natsar da kanta kuma ta tsaya a guri 1, sai dai budurwar tayi kokarin tarwatsa bikin, shi kuma mijin ya nuna amaryar tafi komai mahimmanci a yayin da ya tsaya gefen ta.

Sai dai ba mu tabbatar ba ko ma'auratan sunn gama bikin lafiya ko ba'a gama ba.?

Asali: Legit.ng

Online view pixel