Daga karshe: Buhari yayi magana a Fulani Makiyaya

Daga karshe: Buhari yayi magana a Fulani Makiyaya

- Shugaba Muhammadu Buhari yace akwai hujjan cewa mutanen kasar Mali da Libya sun saje da Fulani makiyaya

- Yace wannan ne sanadiyar hayaniyan da ke faruwa tsakanin makiyaya da mutan gari

Daga karshe: Buhari yayi magana a Fulani Makiyaya
President Buhari

Shugaba Buhari ya daura laifin rikicin makiyaya a fadin kasa akan sajewan da wasu yan kasan Libya da Mali sukayi da su.

Jaridar DailyTrust ta bada rahoton cewa game da cewar shugaba Buhari, yan makaman da yan kasashen afirkan suka kawo ne ake amfani da shi wajen tayar da tarzoma.

KU KARANTA: An kai hari gidan Mamman Daura a Kaduna

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban makarantan National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS), Kuru, da ke jihar Flato.

Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya wakilci shugaba Buhari yace akwai hujjan da ke nuna yadda yan bindigan ke guduwa daga kasashen Mali da Libya da makamai kuma suke zaune da yan Fulani a nan Najeriya.

Amma, yayi gargadin cewa bazaá amince da tayar da tarzoma kowani iri ba a kasan nan.

A bangare guda, wasu yan Fulani makiyaya sun kai hari karamar hukumar Kuje da ke Abuja inda suka kasha mutane 3 ,kuma sukayi garkuw da mutane 10.

Game da cewar Jaridar Daily Sun, makiyayan sun kai hari kauyen Darka ne a ranan lahadi,13 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng