Buhari ya roki yan bindigan Niger Delta
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya na kashe dala biliyan 22 a duk shekara gurin shigo da alkama, shinkafa, sikari da kuma kifi amma idan yan bindiga suka sauke makamansu suka kuma koma gona, abubuwa zasu canja kan tattalin arziki
- Buhari yace aiki tare da gwamnati ta wannan fanni zai ceto matasa daga rashin aiki, kare al’umma, ci gaban zaman lafiya da kuma hannun jari da Karin kudin shiga a jihohin Niger Delta.
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya roki yan bindigan Nigerr Delta da s daina fashe-fashen bututunan mai su kuma rungumi zaman lafiya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kasa yayi wannan roko ne a ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba a grin taron cikar kamfanin man Agip ashekaru 20 a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
KU KARANTA KUMA: Dan shekara 60 yayi wa budurwa fyade a Abia (hotuna)
Shgaban kasar, wanda ministan jiha kan harkan noma da ci gaban karkara Sanata Hwineken Lokpobiri ya wakilce shi, yace yan bindigana s rungumi zaman lafiya da kuma mayar da hankali a kan aikin noma don daidaituwar ci gaban tattalin arziki da samar da dukiya.
A yan makonni da suka wuce, kokarin da gwamnatin tarayya tayi don gannin ta samu yan bindigan sn daina lalata bututunan mai bai yi nasara ba duk da tattaunawa da akeyi a tsakanin kungiyoyin guda biyu.
Yan bindigan sun yi ikirarin cewa dalilin su na kin dakatar da fashe-fashen ya kasance saboda suna son dakatar da gwamnati daga daukan su da rashin muhimmanci a lokacin tattaunawan. Zuwa yanzu, dattawan Niger Delta a tattanawa sun ba gwamnatin tarayya bukatun su.
Ku biyo shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa.
https://youtu.be/D_Sg8sXjJcM
Asali: Legit.ng