Atiku ya daura laifin kisan dan shekara 7 a kan tsarin shari’an Najeriya

Atiku ya daura laifin kisan dan shekara 7 a kan tsarin shari’an Najeriya

- Lokacin da yan Najeriya suka tsaya karshe don ganin shugabannin su sun maida martani ga rahoto da aka kawo na kisan wulakanci da akayi wad an shekara 7 kan yayi sata, Atiku ya maganta kan lamarin

- Yan Najeriya da dama su ga laifin siyasar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ke da alhakin abunda yaron ya aikata

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya maida martani ga zargin kisan jahilci da akayiwa dan shekaru bakwai a jihar Lagas.

Ana zargin cewa yan zanga-zanga sun kona sannan suka kashe Yaron wanda shekarunsa ya zamo abun cece-kuce, saboda yayi yunkurin satan garin rogo.

Atiku ya daura laifin kisan dan shekara 7 a kan tsarin shari’an Najeriya
Dan shekara 7 da aka kona saboda ya saci garin rogo

Bidiyo da hotunan yaron da aka kashe ya tunzura yan Najeriya da dama kuma yan Najeriya sun sun nuna fushinsu da martani a kana abun.

Wasu yan kasa sun soki shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yaron ya yanke hukuncin satan abinci ne saboda yana tsananin jin yunwa.

Atiku wanda ya cika shekaru 70 ya je shafinsa na twita don yayi Magana a kan tsarin hukuncin kasar.

KU KARANTA KUMA: Shaida ya tona asirin Fayose a shari’ar rashawa da ake ciki

Yace ya yi bakin ciki sosai da al’amarin kuma ya nace cewa dole tsarin adalci ya zama irin wanda mutane zasu amince da shi.

https://youtu.be/TOsEY6WVCvo

Asali: Legit.ng

Online view pixel