Hotunan jana’izar marigayi Ibrahim Dasuki
1 - tsawon mintuna
Marigayi Alhaji Ibrahim Dasuki shine sarkin Musulmi na 18, wanda a shekarar 1996 ne gwamnatin mulkin soja ta janar Sani Abacha ta tsige shi daga sarautan sa.
Kafin zaman sa Sarkin musulmi, Dasuki ya taba zama Baraden Sakkwato, kuma aminin tsohon Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardauna.
KU KARANTA: Shin Buhari zai kyale Dasuki yaje ta’aziyyar Mahaifinsa?
Alhaji Dasuki ya rasu a ranar litinin 14 ga watan Nuwamba a wani asibiti a garin Abuja. ga wasu hotunan jana’izar sa da aka yi a jihar Sakkwato inda aka binne shi a Hubbaren shehu Usmanu Danfodio.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng