Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu

Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu

Daya daga cikin wasu Jarirai yan biyu da aka haifa a kwanakin baya dake dauke da wata halittan mai ban al’ajabi, ta rayu.

Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu

Ita dai wannan jaririya an haife ta ne da kwakwalwarta a waje, tun a lokacin da aka haifeta ne aka gano jaririya Aniyah tana da wani ciwo mai suna ‘Encephalocele’ wanda hakan ya sanya kasha goma cikin dari na kashin kai kadai take da shi.

Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu

Da fari dai wasu likitoci sun fada ma iyayen Aniyah cewar ba zata rayu ba, sai dai yayin da ta kai kwana daya a duniya sai aka yi mata tiyata, amma duk da haka aka ce ba zata rayu ba.

KU KARANTA:Matimakin Gwamna ya raba fadan direbobi

Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu
Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu

An sallame Aniyah daga asibiti kwanaki 6 bayan anyi mata tiyata. A satin daya gabata ne Aniyah da yar’uwarta Sophia suka cika watanni hudu a rayuwa, inda mahaifiyarsu ta nuna farin cikin karin samun lafiya da Aniyah keyi, tace Aniyah na yin duk abinda likitoci suka ce ba zata iya yi ba, ma’ana dai Aniyah ta zama gagarabadau.

Jaririyar da aka haifa da kwakwalwarta a waje ta rayu

“Aniyah tana iya daga wuyanta hart a kalli mutane, tana murmushi, tana dariya, tana son waka, kai har ma ta kan yi rawa da jikinta,” inji mahaifiyar.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel