Masoya sun bata kan kujerar Jirgi
Wani Saurayi dan Najeriya ya rabu da budurwarsa wai don bai biya mata kudin babban kujerar Jirgin sama ba yayi tafiyarta zuwa hadaddiyar daular larabawa, wato kasar Dubai.
Saurayin mai suna Sanjay ya bayyana yadda rashin godiya na budurwarsa Tara ya kawo karshen soyayyarsu sakamakon ya siya mata karamin kujeran Jirgi don zuwa kasar Dubai da kudinsa ya kai N500,000 inda ita kuma ta raina, wai ita tafi son ya biya mata kudin babban kujera ko na tsakiya.
KU KARANTA: Ta fado daga bene hawa 9, bayan sharholiya da Saurayinta
Cikin hirar da Sanjay yayi da abokinsa mai suna Dian, Sanjay ya bayyanama masa cewar ba zai iya biya mata kudin kujerar daya haura N500,000 ba musamman yadda ake cikin halin matsin tattalin arziki, wanda yace shine musabbabin daya sanya budurwa tasa rabuwa dashi.
Ga dai yadda hirar ta kasance:
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng