Ya kamata maza ma su kasance a kitchen – Babangida Aliyu
- Tsohon gwamnan jihar Niger Dr Muazu Babangida Aliyu yace ya kamata ace maza ma su kasance a kitchen bisa ga koyarwar Al Quar’ani mai tsarki
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa bisa ga koyarwar musulunci mazaje ne ya kamata suje kasuwa suyi wa mata siyayya
- Aliyu yace mata kawai zasu kasance ne a uwar daki
Tsohon gwamnan jihar Niger, Dr Muazu Babangida Aliyu, ya bayyana cewa maza ma na da rawa da ya kamata su taka a kitchen, bisa ga littafi mai tsarki Al Qur’ani.
Da yake jawabi a garin Minna a karshen mako a gurin taron NDEDIL na shekara-shekara wanda makarantar kimiya ma Negate college of Technology na jihar Niger ta shirya, Aliyu ya bayyana cewa duk da cewan gurbin mata na iya kasancewa a kitchen amma “maza ma na da gurbi a kitchen.”
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya 490,000 zasu samu aiki a sabon shirin Buhari
Babu shakka Aliyu na maida martani ne ga furucin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a kan matarsa a watan Oktoba wanda ya janyo martanai da dama daga jama’a.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa a koyarwar addinin musulunci mazaje ne ya kamata suje kasuwa suyi wa mata siyayya.
Ya ambaci wasu sashi na umurnin musulunci dake cewa: “A zahirin gaskiya maza ne zasu kasance a kitchen kamar yadda Al Qur’ani mai tsarki ya tanadar.
“matan kawai zasu kasance a uwar daki ne.”
Yayi bayanin cewa maza ne zasu biya dukkan bukatun mata kamar irin siyayya daga kasuwa don amfanin iyali saboda “addinin musulunci bai yarda mace ta dunga fita ba bisa tsari ba, ya kamata ace suna cikin gida suna kula da yara.”
KU KARANTA KUMA: Buhari, Donald Trump zasu halarci jana’izar Cif Offor
Aliyu ya kuma bayyana cewa a wannan hali na koma bayan tattalin arziki, ya kamata ace mata da mijin sun tallafa wa juna saboda inganta iyalansu da kasa.
Ya kuma bayyana cewa lokacin auren mata da yawa ya wuce saboda wadanda ke fakewa da addini suna aikata haka suna da jahilcin abunda ya tanadar.
https://youtu.be/WXqU56wXM6M
Asali: Legit.ng