Muna bukatar aiki tukuru da juriya domin cin Ondo - Oyegun
- Basarake John Odigie-Oyegun, shugaban Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa yace jam'iyyar mai mulki zata doke Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan Ondo da za'a yi
- Oyegun yace jihar Ondo nada muhimmanci ga gwamnatin tarayya, dalilin da yasa APC zata amshe jihar daga PDP a shekarar 2017
- Shugaban na kasa yace, dan takarar APC a zaben mai zuwa Rotimi Akeredolu (SAN) nada muhimmanci ga shugabannin jam'iyyar na kasa
Gabannin zaben gwamnan jihar Ondo wanda za'a yi ranar 26 ga Nuwamba, basarake John Odigie Oyegun, shugaban All Progressive Congress (APC) na kasa ya ce jam'iyyar mai mulki zata doke Peoples Democratic Party (PDP) .
KU KARANTA: SHARHI: Dalilai 5 da suka sa Trump ya yi nasara
Yayin da yake kampen na APC domin zaben gwamnan ranar Alhamis 10 ga Nuwamba a Akure, Ohegun yace jihar Ondo nada muhimmanci ga gwamnatin tarayya, abinda yasa ke nan ya zama dole ga APC ta amshi mulki daga PDP cikin shekarar 2017.
Shugaban na kasa yace dan takarar APC a zaben Rotimi Ameredolu yana da daraja ga shugabannin jam'iyyar na kasa.
Gangamin ya sami halartar sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, gwamnonin Ogun, Plateau, Borno,Benue, Sokoto da Bauchi, Ibikunle Amosun, Salamon Lalong, Kashim Shetima, Samuel Ortom, Aminu Tambuwal and Mohammed Abubakar.
Ku biyo shafinmu na Tiwuta: @naijcomhausa
Asali: Legit.ng