Sheikh Sunusi Gumbi ya rasu
1 - tsawon mintuna
Shahararren malamin addinin Islama dake zaune a Kaduna Sheikh Ahmad Sunusi Muhammad Sunusi Gumbi ya rasu.
Wata majiya daga iyalan shehin Malamin ta bayyana cewar malamin ya rasu ne a wani asibiti dake garin Abuja da misalin karfe 10 na daren jiya Alhamis 10 ga watan Nuwamba bayan yayi fama da rashin lafiya.
KU KARANTA:Kan wayar wuta ya caki kan Jariri
Sheikh Gumbi ya rasu ya bar mata biyu da yaya da dama, da jikoki masu yawa.
Zai’a yi jana’izarsa yau bayan sallar Juma’a a masallacin Sultan Bello dake Unguwar Sarki.
Allah ya jikan sa da rahama, Amin.
Asali: Legit.ng