Darajar farashin Naira na N460 a kasuwar canji

Darajar farashin Naira na N460 a kasuwar canji

Darajar farashin Naira ba ta sauka ba a Kasuwar canji

A jiya, Alhamis, Dalar Amurka tana kan N460 a Kasuwar canjin kudi

A yanzu haka, Dalar Amurka ta fadi bisa Naira cikin ‘yan kwanaki

Darajar farashin Naira na N460 a kasuwar canji

 

 

 

 

 

 

 

Darajar farashin Naira ta samu yunkurawa a kasuwar canjin kudi na Najeriya. Kudin Naira na Najeriya ya samu dagawa da abin da ya kai N5 a kasuwar canji, a wannan makon. Inji Hukumar Dillacin labarai na Kasa watau NAN

A kwanakin baya an canza N465 kan kowace Dalar Amurka guda, yanzu kuwa ana saida Dalar ne a kan N460. Ma’ana dai Naira ta kara daraja da Naira 5. Har kuma karshen wannan makon Naira ba ta fadi daga inda take ba.

KU KARANTA: Rashin kudi: Shugaba Buhari ya dauki wani mataki

Masana sun ce abin da ya sa farashin Naira yayi kikam shine kudin da Bureau de Change suka samu cikin ‘yan kwanakin nan. Babban Bankin Kasar ya dauki wani mataki da suka sa dala ta kara yawa a cikin kasuwa. Hakan kuwa zai sa Naira ba za tayi kasa da N475 kan kowace dala duk rintsi.

Malam Aminu Gwadabe wanda shine Shugaban ‘Yan Canji na Kasar yace Bankin CBN ya kyauta ta zai rika sa Bureau De Change su samu dala. Gwadabe yace duk kusan farashin daya ne da CBN, hakan ya rage tazarar da ake samu da tsakanin Babban Banki da ‘Yan bunburutu. Shugaban ‘Yan Canji na Kasa watau ABCON ya gargadi masu boye Dalolin Amurka sai sun tashi sun fitar.

Ku biyo mu a shafin Twitter, shine: @naijcomhausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng