Buhari ya hana ma’aikata shiga sahun farko na Jirgi

Buhari ya hana ma’aikata shiga sahun farko na Jirgi

- Gwamnatin tarayya ta hana dukkanin ma’aikatan ta kama sahun farko na Jirgi

- Bai hallata Ministoci, sakatarori da sauran ma’aikatan gwamnati su shiga sahun farko na Jirgi ba

- Gwamnatin Kasar na kukan rashin kudi

Buhari ya hana ma’aikata shiga sahun farko na Jirgi
Shugaba Buhari ya hana hawa babbar kujera

 

 

 

 

 

 

 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta hana ma’aikatan Gwamnati shiga sahun farko na Jirgin sama wajen tafiya. Gwamnatin Shugaba Buhari tace daga yanzu ka da wani Jami’in Minista, Sakatare, Hafsun Soji, ko masu ba Shugaban Kasar shawara da ya kara kama sahun gaba na jirgin sama wajen tafiya.

Jaridar The Cable tace Shugaba Buhari ya dauki matakin haramta hawa sahun farkon na jirgin sama ne domin matsalar tattalin arziki da Najeriya ta ke fuskanta. Gwamnatin Shugaba Buhari tace daga yanzu bai halatta wani Jami’in Gwamnatin Tarayya ya shiga sahun farko na jirgin sama; ko a cikin Kasar ne ko a Kasar waje. Kujerar Sahun farko watau babban kujera na jirgin sama dai ya fi tsada.

KU KARANTA: An ja kunnen Shugaba Buhari

A baya dai cikin watan Afrilun shekarar nan, Shugaba Buhari ya hana Ministocin sa kama sahun farko na jirgin saman. Sai dai Jam’iyyar PDP mai adawa tace duk zance ne kawai Shugaban Kasar yake yi, domin kuwan an hangi Ministan Labarai da Al’adu, Lai Muhammad a cikin wani jirgin yawo.

Yayin da Najeriyar ke fama da matsalar tattalin arziki, kasar za ta karbi Biliyan $5 daga Manyan Kamfunan mai da ke Kasar nan bisa yarjejeniyar da suka yi a baya. Wannan rahoto ya fito ne daga daga Jaridar Financial Times.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel