Shin kana yawan shanya kaya a wajen da babu rana, toka dain

Shin kana yawan shanya kaya a wajen da babu rana, toka dain

- Yana da kyau masuyin shanya a inda babu rana su daina, musamman cikin daki ko baranda

- Domin kuwa wani sabon ilimin da aka samu yin hakan yakan janyo ma mutum wani babban matsala musamman idan mutum yana da matsalar shanyewar jiki kokuma asma

Shin kana yawan shanya kaya a wajen da babu rana, toka dain

A kwanakin bayane dai aka samu wani mutum a garin Boston ya kamu da matsalar sassan numfashin jikinsa sun lalace sakamakon kayan da yake shanyawa a cikin daki ko wani wajen da babu rana.

Craig mather wanda dan shekara 34 ne da haihuwa an dai bayyana cewar yana da Pulmonary Aspergillosis, inda likitan ya rubutamasa maganin nan mai suna Antimicrobial inda yace nan bada dadewa ba zai samu lafiya.

Inda likitan ya kara bashi shawaran daya daina shanya kayan sawan sa a cikin gidan sa, Craig y dauki shawaran likitan kasan cewar yana da yara uku, kuma yana son yaga girman yaran. Bayan shekara guda sai Craig ya tabbatar da ya samu lafiya sosa bayan dayabi shawarar likitan nashi.

An dai bayyana abun ne da cewar busassun kayan suna komawa ne cikin dakin kwanan mutum inda suke komawa jikin dan Adam daga baya, haka kuma masu matsalar asma da kuma matsalar numfashi suna saurin kamuw da irin wannan matsalar ta shanyan kaya a cikin daki.

Haka ma mutanen da suke da cutar HIV ko kuma wa'anda akayi musu Kemo suma duk zasu iya kamuwa da wannan cutar ta Pulmonary Aspergillosis. Wannan cutar yanada saukin kama mutum kuma nan da nan yake batama mutum hanyoyin numfashin jikin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng