Tusa na hura wuta: Wata mata ta kone da tusa

Tusa na hura wuta: Wata mata ta kone da tusa

- Ashe da gaske ne da ake cewa tusa na hura wuta, yau tusa ta tada wuta

- Abin mamaki; wata mata tayi tusa yayin da ake yi mata aiki asibiti, hakan kuwa ta jawo gobara

Iskar tusa ta hade da kayan aikin wuta a asibiti, hakan ya sa wannan mata ta kone

Tusa na hura wuta: Wata mata ta kone da tusa

 

 

 

Abin mamaki ne Malam Bahaushe yayi gaskiya, ashe da gaske ne da ake cewa tusa na hura wuta, yau tusa ta tada wuta. A Kasar Japan wani abin mamaki ya faru a wani asibiti, inda tusa ta tada wuta yayin da ake wani aiki. Likitoci kawai sai suka ga wuta na tashi ana tsakiyar fede wannan mata a asibiti.

Wannan abu ya faru ne a Kasar Japan, a wani Asibitin koyon aiki da ke Tokyo. Likitoci suna tsakiyar fede wata mata da na’urar Laser mai kamar wakilya, sai gobara ta barke, kuma ba wani abu ne ya jaw gobarar ba sai tusar da matar tayi yayin da ake yi mata aiki.

KU KARANTA: Ta gyaru ga Masu cin kwadi a Kano

An dai samu matsala ne lokacin da wannan mata da ake yi wa aiki ta saki tusa, iskar tusar ta sa wuta ta tashi a nan take. Su kan su likitocin da fari, sun rasa gane abin da ya faru. Sinadarin da ke cikin tusar ta hade da na’urar Laser, wannan ya sa wuta ta kama.

Wannan abu ya jawo wannan mata mai shekaru 30 ta kone a kafafun ta. Dama can ana mata aiki ne a mahaifar ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng