Zaka bukaci ka kalli wannan mawakun na Amurka
1 - tsawon mintuna
Ance waka yare ce da kowa ke fahimta a duniya ko da kuwa ba da yaren ka akeyin ta ba, kuma ko daga wace duniya kake indai har za Kaji kida, to akwai yiwuwar yin rawa kenan.

Mawaki dan kasar Amurka ba dadewa ya tabbatar da wannan maganar gaskiya ce, ya shirya wani biki mai suna Heneiken Experience wanda akayi a hutun karshen mako tare da cool FM OAP Dutun, kuma bidiyon ya nuna yayi raha sosai.

Shi da Dotun sunyi rawa iri-iri na yan kasar Najeriya kamar shoki da dai sauran su, kuma yayi rawa irin ta su ta yan gayu mai burgewa.
Asali: Legit.ng