Boko Haram sun far ma sojin Operation Lafiya Dole

Boko Haram sun far ma sojin Operation Lafiya Dole

- An kaiwa rundunar sojin Operation Lafiya Dole barno mumunan hari

- Wasu sojoji sun rasa rayukansu kuma an kai Wadanda suka jinkita asibiti

- Rundunar sojin najeriya sun sha alwashin damke yan ta'adda

Boko Haram sun far ma sojin Operation Lafiya Dole
File photo of Nigerian soldiers on the frontline

Wasu rundunar yan tada kayar bayan boko haram sun kashe jami'an sojin najeriya 9 a wata harin da aka kai.

Sun kai harin ne a unguwar Talala da Aljigin a ranan lahadi , 30 ga watan oktoba.

A wata jawabin da kakakin Hukumar sojin ,kanal Kukasheka Usmanyace soji 5, yan banga 3 da mai farin wula 1 ne suka rasa rayukansu. Kana soji 19 sun jinkita da kuma mai farin wula 1.

KU KARANTA: Sojoji sun harbe wani dan Boko Haram zai tada bam

Karanta jawabin:

“Rundunar Operation Lafiya Dole masu yin sharan yan boko haran a kudancin Borno, sun sha ruwan wutan yan kungiyar Boko Haram a kauyen Ugundirin , karamar hukumar Damboa , a jiya.

“Abin takaici, sojoji 5, yan banga 3,da mai farin hula 1 n suka rasa rayukansu yayinda soji 19 ne suka jinkita kuma mai farin hula 1. An kai gawawwakin wadanda suka rasu Maiduguri kuma wadanda suka jinkita na asibiti suna jinya.

“Rundunar sojin sun lalata motar bindigar yan ta’addan kuma sun sami bindigogin sama 2, bindiga mai harba kanta 1, bam 1, bindigan Ak47 1,da kuma harsahai. An tura soji wurin domin damko yan Boko Haram dinda suka arce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng