Gidan dan wasar kwallo Neymar a Rio kayatacce ne

Gidan dan wasar kwallo Neymar a Rio kayatacce ne

Mai daukar albashi na zunzurutun kudi har miliyan  19.8 euro, Neymar dan wasar kwallon kafa na Brazil da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ze iya mallakar duk wani abu mai kyau na rayuwa.

Saboda sannin shi da akayi da yin rayuwa mai tsada da fankama, da son jin dadi, dan kasar Brazil din ya kara da wani katon gida cikin abubuwan da ya mallaka.

Gidan dan wasar kwallo Neymar a Rio kayatacce ne
Neymar

Kamar yadda O Globo suka bayyana, dan wasan na kasar Brazil yayi sabon katon gida a kasar Brazil garin Rio de Jeneiro wanda yake da karamin filin jirgi mai saukar angulu, da gurin yin iyo, da gurin wasar table tennis, da dakuna 6 da mahadar ruwa.

Gidan dan wasar kwallo Neymar a Rio kayatacce ne
Gidan Neymar

Anyi rohoton cewa katon gidan anyi shi a Portobello ,tafiyar awa 1 tsakanin shi da birnin, kuma gidan ya kai girman mita 6,265.

Gidan dan wasar kwallo Neymar a Rio kayatacce ne
Gaban gidan Neymar

Neymar yana da jirgin ruwa mai tsawon mita 25, wanda aka saya kan kudi Miliyan 3.5 euro, da jirgin hawa na miliyan 4 euro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel