Mayan mutane sun halarci auren yarinyar shugaban kasa
Yarinyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Fatima, tayi aure da burin zuciyarta, Mallam Ya’u Kumo a jiya Juma’a, 28 ga watan Oktoba.
Ta shiga gidan auren ne a matsayin mata ta hudu ga Gimba, wanda ya kasance tsohon manajan-darakta na bankin Mortgage na tarayyana Najeriya.
Manyan shugabanninmu da sarakunan gargajiya sun shika sun tunbatsa a gurin daurin auren wanda akayi a gidan Buhari dake Miaaduwa GRA, Daura, jihar Katsina.
Manyan motoci daban-daban wanda ke mallakar yan gayya sun cika garin, wanda yayi sanadiya cunkoson ababen hawa.
KU KARANTA KUMA: Rahama ta fara shirin fim tare da Akon
Kafin a aje gurin taron bikin, yan gayya da dama sun tafi fadar sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk kai tsaye domin su yi gaisuwar ban girma.
Ya bayyana cewa shugaban kasa bai halarci daurin auren yarinyarsa ta biyu ba kamar yadda aka kansa yana sallar Juma’a a masallacin fadar shugaban kasa a jiya.
Asali: Legit.ng