Kin sabawa tarbiyyar Fulani – Matan Adamawa ga Aisha Buhari

Kin sabawa tarbiyyar Fulani – Matan Adamawa ga Aisha Buhari

- Wata kungiyar Matan Adamawa sun siffanta maganan Aisha Buhari a hirar BBC a matsayin shirme

- Kungiyar tace kasancewan ta yar Fulani, bai kamata ta fito duniya tana bata maigidanta ba

- Matan sun soki Aisha da cewa tana bata sunan ta a matsayin uwargidan shugaban Kasa

Kin sabawa tarbiyyar Fulani – Matan Adamawa ga Aisha Buhari

Wata kungiyar Matan Adamawa sun cu Aisha Buhari ta sabawa tarbiyyar Fulani game da maganar da tayi akan mijinta,shugaban kasa.

Kungiyar mai suna, Adamawa League of Women Empowerment,tayi Allah wadai da Aisha Buhari ,akan maganar da tayi a hirar BBC akan salon shugabancin maigidanta.

KU KARANTA: Sabuwar Amarya ta rasu a mummunan hadari

Kakakin Kungiyar, Maryam Ibrahim, ya bayyana hakan ne a ranan Alhamis,27 ga watan oktoba a wata hira da yan jarida a yola ,inda tace maganar Aisha ya kaskantar da gidan,kana kuma ya baiwa yan adawa daman sukan Shugaban Kasa.

Game da cewar jaridar Dailypost, Kungiyar tace kasancewan ta yar Fulani, bai kamata ta fito duniya tana bata maigidanta ba

“Akan wannan ne muke ca da maganar Aisha Buhari a irin wannan lokaci. Kana wannan Magana nata ya sabawa tarbiyyar, Pula’aku,mutunci da dabi’ar fulbe.

Kungiyar ta kara da cewa ba’a taba samun matar shugaban kasa tayi batanci ga mijinta ba , kuma wannan abun da Aisha tayi,batanci ne ga fadar shugaban kasa.

Matan sun jaddada goyon bayansu ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yunkurinsa na kawo gyara kasa.

 “Hakazalika, muna jaddad goyon bayanmu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a yunkurinsa da kwato mutunci Njaeriya a matsayin gwarzon Afrika.Kungiyar tace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng