Ana zargin sarauniyar kyau ta jihar Anambra da aikata madigo

Ana zargin sarauniyar kyau ta jihar Anambra da aikata madigo

A lokacin da muke tunanin mun ga karshen wannan ba’a, abun kunya da ya nuna sarauniyar kyau na Misis Anambra na shekara 2015, Chidinma Okeke, masu bankade sunce bamu daina ba.

Ana zargin sarauniyar kyau ta jihar Anambra da aikata madigo
Sarauniyar kyau ta jihar Anambra Chidinma

Bayan bidiyon yayi fice a yanar gizo na dan wani lokaci, Chidinma ta fito ta karyata cewan ba ita bace a bidiyon. Ta nace kan cewa an yi amfani da fuskarta ne a na wata. Ta rubuta:

“An janyo hankalina zuwa wani hoto da bidiyo dake yawo a yanar gizo inda akayi amfani da fuskata a na wata dake aikata masha’a ta hanyar fasaha na wani abun hada hoto. Wannan shirin makircine da wasu makiyana suka shirya don kawai su bata mun suna da kuma alkawarin bata mun baiwata ta hanya mafi muni. Ina so nayi amfani da damar nan gurin bayyana cewa wannan hoto bani bace.

Kara karanta wannan

Mata sana'a ta fi bani: Yadda mata ta gina gidaje da sana'ar toya 'Masa' a Gombe

 “Ni mutunce da ta taso daga gidan mutunci. Don haka bazan iya aikata irin wannan ta’asar ba. A halin yanzu na mika al’amarin ga lauya na domin a hukunta wanda ya haddasa wannan mugun ta’asar da da’awar. Don Allah ina shawartanku da kuyi watsi da wannan hoto da bidiyo da kuma daukar shi a matsayin aikin makiya. Nagode. Okeke Chidinma.”

Amma da yawan mabiyanta basu da wani masaniyan akan haka kamar yadda suke tunanin tana yawo da hankalinsu ne.

A halin yanzu, ba’a san wanda ya shirya makarkashiyan ba kuma ba’a san dalilin da yasa maishi ya saki bidiyon da ya kamata ya zamo sirri ba. Yan bani na iya sunyi ikirarin cewa wanda ya shirya makircin makusancin Chidinma ne. kuma maishi ya saki bidiyo na biyu wanda bai fito da kyau ba, ya nuna fuskar sarauniyar kyan da mataimakiyar ta. Bidiyon ya dau kimanin sakan 59.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng