Yarinyar Buhari, Fatima na shirin Aure
Yarinyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biyu, Hajiya Fatima na shirin auren tsohon manajan-darakta na bankin Mortgage na tarayyan Najeriya, Malam Gimba Yau Kumo.

Za’ayi bikin ne a ranar juma’an nan 28 ga watan Oktoba a jihar Katsina.


Fatima ta kasance yarinyar shugaban kasa Buhari ta biyu daga matar sa ta farko Safinatu Muhammadu Buhari.
KU KARANTA KUMA: Nagoyi bayan Buhari dari bisa dari- John Okafor
Shugaban kasar Najeriya ya auri tsohuwar matarsa, marigayiya Safinatu Muhammadu Buhari a shekara ta 1971 tana da shekaru 18 da haihuwa, an haife ta a ranar 11 ga watan Disamba ta shekarar 1952, a cikin zuri’ar Fulani kuma tana da nasaba da Shehu Usman Danfodio.
Sun samu yara biyar da juna, Zulaiha (Marigayiya), Fatima, Musa, Hadiza da kuma Safinatu Buhari.
Asali: Legit.ng