Yan Real Madrid zasu ji dadin wannan

Yan Real Madrid zasu ji dadin wannan

- Kyaftin din Barcelona Andres Iniesta zai yi jinyar mako shida zuwa takwas sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa a wasan da suka doke Valencia.

- Dan wasan na tsakiya ya ji rauni ne a lokacin da suka yi taho-mu-gama da Enzo Perez a minti 14 da soma wasan da aka tashi da ci 3-2, ida aka dauke shi a gadon daukar marasa lafiya.

Yan Real Madrid zasu ji dadin wannan

Mai yiwuwa ba zai buga sauran wasannin da za a yi na gasar cin kofin zakarun turai ba, kuma ba zai buga karawar da za su yi da Manchester City ranar daya ga watan Nuwamba ba.

Barca ta yi nasara a wasan ne sakamon kwallon da Lionel Messi ya ci bayan sun samu bugun fenareti.

Haka kuma 'yan wasan Barca biyu -- Gerard Pique da Jordi Alba -- ba za su buga wasan da kungiyar za ta yi da City ba saboda raunin da suka ji.

A wani labarin kuma, Real Madrid ta samu nasara a kan Athletic Bilbao da ci 2-1 a gasar La Liga wasan mako na tara da suka fafata a ranar Lahadi.

Karim Benzema ne ya fara ci wa Madrid kwallo a minti na bakwai da fara tamaula, kuma a minti na 28 Bilbao ta farke ta hannun Sabin Merino.

Saura minti takwas a tashi daga wasan Alvaro Morata ya ci kwallo na biyu, wanda hakan ya bai wa Madrid damar samun maki uku a fafatawar.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta dare mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 21, Sevilla ce ta biyu da maki 20, sai Barcelona mai maki 19 a matsayi na uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel