Jami’ai sun yi ram da wata mata dauke da kwayar koken
– An kama wata mata ‘Yar Najeriya dauke da kwayar koken watau hodar iblis
– Jami’an Binciken kwayayoyi na Kasa, NDLEA sun kama wannan mata dauke da kusan rabin kilo na kwayar koken
– Misis Ijeoma ta kulle hodar iblis din ne cikin rigar mama
An kama wata mata mai shekaru talatin dauke da Hodar Iblis wanda aka fi sani da kwayar koken a Legas. Wannan mata tana dauke da kusan giram 500 na kwayar Koken din daure cikin ‘yar rigar mamar ta a Ranar Jumu’ar nan ta jiya.
An yi ram da Misis Nnaji Ijeoma ne a Filin saukar jirgi na Murtala Muhammad da ke Birnin Legas. An gano cewa wannan mata tana dauke da wani farin garin sinadarin da ake zargi hodar iblis din ne a cikin rigar mamar ta a boye, da aka bincika sai aka gano wannan mata na dauke da kwayar koken.
KU KARANTA: Yarinyar da aka haifa sau biyu a duniya
Wannan mata ta fallasa cewa anyi mata alkawarin Naira Miliyan daya idan har ta sauke wadannan kwayoyi a Najeriya. Misis Nnaji Ijeoma wanda asalin ‘Yar Enugu ce tace an bata wannan kaya ne daga Kasar Brazil, ita nata kawai ta kawo su Najeriya.
Mai magana da bakin Hukumar NDLEA mai yakar harkar kwayoyi ta Kasa ta bayyana cewa an samu wannan mata ne dauke da giram 535 na Hodar Iblis ko Kwayar Koken a kunshe cikin rigar mamar ta. Misis Nnaji Ijeoma tace tana fama da matsalar rashin kudi ne shiyasa tayi wannan aiki.
Asali: Legit.ng