Mabiya nagari: Matsalar Najeriya

Mabiya nagari: Matsalar Najeriya

Daga Edita: Kwanan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da "canji ya fara da ni", wanda manufarsa itace kawo da'a da kishin kasa ga 'yan Najeriya

Nicholas Oluwaseyi, marubucin Legit.ng

Ya yarda da shugaban dake cewa matsalar Najeriya bata rashin shugabanci nagari bane, a'a rashin mabiya nagari ne, Mista Oluwaseyi ya zana dabi'u bakwai na mabiya kyawawa.

"Duk tsawon rayuwata har zuwa yanzu, ni kanji karin magana mai cewa - "Ka zama shugaba nagari" fiye da wanda ke cewa - "Ka zama mabiyi nagari".

Na karanta litattafai da dama game da shugabanci, amma 'Yan kadan ke akwai game da mabiya. Na sami shawarwari kan yadda zan zama shugaba nagari, amma, kadan ne daga cikin masu bani shawara suka koya mani yadda zan iya zama mabiyi nagari.

Kowanen mu na son zama shugaba nagari, amma ba mai son zama mabiyi nagari, wanda yafi kawaici a cikin mu so yake ya zama "sugaba mai bautawa", ba wai kawai mai bauta ba. Idan muna son ci gaba, dole ne mu kawo maganar mabiya. Kowa nada 'yanci a cikin al'umma, amma babu mai son daukar dawainiya".

KU KARANTA: An kusa fara bikin cika shekaru goma da hawan Sarkin Musulmi

Ga halaye masu kyawu na mabiyi nagari:

1. Sanin ya kamata: Daukar umurni na da kyawu, amma mutun yayi aiki da hankalinsa wajen tantance umurnin da baya da kyawu da wanda yake mai kyaw

2. Mabiya nagari, sune ma'aikata nagari, masu kishi da maida hankali kan aikinsu. Hakkin su ne su zama ma'aikata nagari

3. Kwarewar: wasu lokutta ana samun tangarda domin mabiyin bai kware ba kan aikinsa

4. Gaskiya: Ya zama wajibi mabiyi ya fada ma shugaba matsayin kokarin da shugaban ke yi da kuma hanyar da ya dauka na cin nasara

5. Jaruntaka: Mabiya nada hakkin gaya ma shugabanni gaskiya, kuma suna da bukatar kasancewa jarumai su fadi gaskiya

6. Basira: wani karin magana lokacin yakin duniya na biyu mai cewa "sakakken baki mai nutse jiragen ruwa". A takaice,'mutum ya san irin maganar da ke fitowa bakinsa

7. Biyayya: Mabiyi nagari nada hakkin biyayya ga jama'arsa. Mabiya wadanda basu da biyayya matsala ne ga jama'a

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng