Derya B mai kimanin shekaru 15 ta mutu gurin haihuwa

Derya B mai kimanin shekaru 15 ta mutu gurin haihuwa

A gabashin Turkey, wata matar aure mai kimanin shekaru 15 da haihuwa mai suna Derya B ta mutu sakamakon ciwon kwakwalwa daya kamata alokacin da take kokarin haihuwa.

Derya B mai kimanin shekaru 15 ta mutu gurin haihuwa

Derya B yar shekara 15 kenan data mutu sakamakon ciwon kwakwalwa daya kamata alokacin da take kokarin haihuwa

Andai bayyana cewar an matsama yarinyar ne da tayi aure alokacin da take da shekara 14 da haihuwa a duniya, inda nan da nan ta samu ciki, inda tayi auren bisa addininta, inda daga baya tace ga garin ku a asibitin kudi na Batman dake yammacin Turkey a ranar Lahadi 17 ga watan Oktoban wannan shekarar sakamakon haihuwa da yazo mata.

KU KARANTA KUMA: Buhari be da masaniya kan yadda aka saki yan matan chibok

Haka kuma, 'yan sandan dake yankin suna gudanar da bincike dangane da mutuwar matashiyar matar auren.

Acewar kwararren likitan mata mai suna Farfesa M.D Aydan Biri, ya bayyana cewar, yanada matukar hatsari karamar yarinya mai karancin shekaru ta dauki ciki sakamakon wasu halittun jikinta da basu gaba budewa ba, wanda yace babu mamaki irin wannan abun ya faru da wannan yarinyar.

Allah ya jikanta!

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng