Anci mutuncin sarauniyar kyau

Anci mutuncin sarauniyar kyau

Sarauniyar kyau ta jahar Imo da taci ba ba dadewa Stephenie Korie, kwana 2 da suka wuce wani soja yaci mutuncinta ya mareta a bikin kamalla karatun kawayenta.

" Kasar Najeriya ta koma wani abu daban, a inda mazaje basa daraja mata, ina jin takaicin sojojin Najeriya, basa ganin darajar mata, ina jin abubuwan da suke iri-irin haka a jahar Abia, garin Aba, amma ban gama yarda ba sai da abun ya faru akaina.

A hakikanin gaskiya na tafi bikin kamalla makaranta na kawayena da kanwata a makarantar mu, sai kawai ba zato wasu samari suka tada fada, sai naji banda natsuwa, sai nace ma kanwata mufita, sai kawai wani yazo ya sha gabanmu(sojane amma bai sa kaya ba), sai ya tambaye ni tare da suwa nake.

Anci mutuncin sarauniyar kyau
Stephenie Korie

" Nayi mamaki saboda gayyata ta akayi, kuma ban wani sanin mutane da yawa a gurin ba, amma lokacin ban bashi ansa ba, sai kawai yace ze mare ni in ban fada mai ba, nayi mamaki sai na tambaye shi dalili?

KU KARANTA KUMA: Buhari be da masaniya kan yadda aka saki yan matan chibok

Kafin in san me ke faruwa, kawai sai naji saukar mari a kunci na, yanzu ina mamaki, dama haka maza suke marin duk macen da suka gani?

Ko mazajen kasar nan basa ganin darajar mata? Wannan babban abun kunyane ga sojojin kasar nan, dan suna yin abunda be dace ba, kuma da aka tambaye shi dan me ya maran, sai yace "wai an san ko shi waye"

Mutashi tsaye dan dena cin mutun cin da sojoji keyi, Maza su dena dukan mata ba dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng