Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus

Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron kasuwanci ya kuma gana da wakilin yan Najeriya a Berlin kasar Jamus a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba.

Shugaban kasa Buhari tare da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, gwamnan jihar Imo Rochas Okorochas, shugaban kungiyar majalisar dattawa a harkan tsaro Sanata Ahmed Lawan da ministan cikin gida Abdulrahman Dambazzau a ziyarar aiki da ya kai kasar Jamus a ranar 14 ga watan Oktoba.

Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus
Shuagabn kasa Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus
Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da jami'ansa a kasar Jamus
Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus
Shugaban kasa Buhari, Gwaman jihar Borno Kashim Shettima, Gwamnan jihar Imo Rochasa Okrochas, da sauran jami'ansa a gurin taron
Shugaba Buhari ya halarci taron kungiyar kasuwanci a Jamus

KU KARANTA KUMA: Ahmadu Ali ya aurar da yarsa

A jiyan ne kuma shugaban kasa Buhari wanda ya isa kasar Jamus a ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba, don ziyarar kwanaki uku ya gana da Merkel a ofishinta dake Berlin a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba.

Inda kasar ta hada rundunar sojoji inda suka jira shugaban kasar Najeriya domin yi masa maraba na musamman. Shugabannin kasashen guda biyu sun kana kan yadda zasu kawo ci gaba a kasashen nasu ta hanyar hadin gwiwa.

Sun zanta kan muhimman batutuwa irin hanyar inganta tsaro, bada tallafi ga yan gudun hijira da kuma sabonta yankin arewa maso kudu, sannan kuma sun tattauna kan yadda za'a inganta harkan kasuwanci a tsakanin kasashen guda biyu.

Gamuwar yana sa ran kara dangon zaman lafiya tsakanin kasashen guda biyu, zasu magance matsalar tsaro da kuma inganta hanun jarin kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng