Rikicin kungiyoyin asiri: An kashe mutum da budurwarsa
Wasu yan kungiyar asiri sun kashe abokin gabarsu da budurwarsa dukkaninsu yan aji biyu daga tsangayar ilimin kasa a jami’ar jihar Binuwe.
Jaridar Leadership ta ruwaito an kashe Solomon Aondoaseer da budurwarsa yar shekaru 20 Doofan Agbaja sanadiyyar gaba dake tsakanin kungiyar asirin Solomon da wata kungiyar asiri ta daban.
Kaakakin hukumar yansandan jihar Binuwe Moses Yamu ya tabbatar da kisa, shi dai Solomon dan wata kungiyar asiri ne mai suna ‘Red Viper’ yayin da su kuma abokan gaban nasa yan ‘Black Axe’ ne. said a Yamu yace an kama wadanda suka aikata laifin, inda yace sun amsa laifukansu.
Wadanda aka kama sun hada da Paul Adum, Terkumbur Gber, Teryila Aondona, Thaddeus Ukaaku da kuma Damian Swem.
KU KARANTA: Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu
Wannan ba shi ne karo na farko ba na yin kashe kashen kungiyoyin asiri a jihar Binuwe ba, ko a nan baya, kimanin watanni hudu da suka gabata, an kai wani hari a jami’ar tarayya ta kimiyyar noma dake jihar inda aka kashe mutane bakwai.
Shidda daga cikin wadanda aka kashen daliban jami’ar ne dake zaune a dakunan yan kasuwa dake farfajiyar makarantar mai suna Shammah Hostel. Cikon na bakwan mai gadi ne.
Moses Yamu yace an dauke gawar mamatan, inda ya tabbatar da cewa kisan daliban ya faru ne sakamakon rikicin yayan kungiyar asiri.
Asali: Legit.ng