Abubuwa 8 da Aisha Buhari ta fada game da gwamnatin mijinta

Abubuwa 8 da Aisha Buhari ta fada game da gwamnatin mijinta

Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.

Abubuwa 8 da Aisha Buhari ta fada game da gwamnatin mijinta
Aisha Buhari tare da mai gidanta

1. Matar shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana cewa gwamnatin mai gidanta Shugaba Muhammadu Buhari ta yi watsi da fiye da rabin mutanen da suka yi mata wahala har ta samu mulki. Domin kimanin mutane miliyan 15 ne suka zabi mijin nata. Don haka ya zama dole yayi taka tsan-tsan da al’amuran mutane.

KU KARANTA KUMA: Ana binciken mai a jihohin Arewa

2. Ta kara da cewa shugaba buhari bai san mafi yawan mutanen da ya nada a cikin gwamnatinsa ba. Domin yawancinsu basu da katin zabe, wasu ma ba’a gansu a gurin yakin neman zabe ba, duk mafi akasarinsu yan tayi dadi ne.

3. Haka kuma ta kara da cewa wasu "'yan tsiraru" ne suke juya akalar gwamnati, inda suke zabar mutanen da ake bai wa mukami. Inda ta bayyana cewa koda dai cewan Buhari ne shugaba amma dole abunda mutane suke so, shi yake yi.

4. Tace: "Cikin wadanda ya zaba ya nada idan an tambaye shi 45 cikin 50 ba saninsu ya yi ba. Bai san su ba. Haka nake zato. Ni ma ban san su ba saboda na zauna da shi shekara 27,"

5. Aisha ta ce duk da cewan ita ba jami’ar gwamnati ba amma zatayi maga a matsayinta na mace uwa, an riga an san cewa bazasu samu shekaru hudunan lafiya ba.

6. Ta kuma bayyana cewan tana gudur masu borin mutane miliyan goma sha biyar dake rataye a wuyansu. cewa kamata yayi aba masu katin zabe mukaman ba wai yan tayi dadi ba, saboda da su basu san me suke so ba, abun dubawane ta yadda idan suka fito yin magana a bainar jama'a sai suke su ba yan siyasa bane.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Boko Haram sun saki wasu yan matan Chibok

7. Mafi aka sarin wadanda aka daura a kan mukamai sune yan ana ruwa gudu, idan aka cire irinsu Fashola Ameachi da sauransu, duk sauran basu san yadda tsarin gudanar da mulki yake ba.

8. Daga karshe tace ya kamata a saurari jama’a domin sune zasu sake zabe, ko da dai shugaba Buhari bai gaya mata cewa zai sake tsayawa takara a shekara ta 2019 ko kuma ba zai tsaya ba. Amma duk da haka mutanen ne dai zasu sake zaben jam’iyyarAPC domin basu fatan abunda ya faru a baya ya maimaita kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng