Sarkin Kano Sanusi yace yana son Yesu Almasihu

Sarkin Kano Sanusi yace yana son Yesu Almasihu

- Sarkin Kano Sunusi Lamido ya bayyana cewan shi musulmi ne amma yana son Yesu Almasihu (Annabi Isa)

- Ya bayyana hakan ne a shafin sa na Instagram

- Yace mutun bazai taba zama cikakken Musulmi ba tare da kaunar Yesu ba

sarkin Kano, Lamido Muhammed Sanusi yace shafin sa na Instagram a safiyar yau don bayyana cewa yana son Yesu Almasihu duk da cewan shi musulmi ne.

ya saka wani hoto tare da taken “mutane da yawa basu san da cewa ba mutun ba zai iya zama musulmi ba, ba tare da yana kaunar yesu ba wanda aka fi sani da Annabi Isa (Alayhis Salam) a larabce.”

Ra’ayi daga mutane ya nuna cewa sun goyi bayan sanarwar da yayi kuma sannan hoton ya nuna kwatankwancin soyayyar mutane 800 ta hanyar alama (Likes) bayan sa’a daya da sa hoton.

KU KARANTA KUMA: Fasto ya hau kan ryuwan cikin wata a coci

Sarkin Kano Sanusi yace yana son Yesu Almasihu
Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi

A kwanakin baya munji cewan Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya karyata rade-raden cewa shi ya taba kai hari ga shuagaban kasa Muhammadu Buhari kan halin da tattalin arziki ke ciki.

Ya bayyana cewa a duk lokacin da yaso ya bayar da suka ga gwamnati, zaiyi ne a bude a kuma cikin hanyar da ta dace amma ba wai ta hanyar kalaman keta a kafofin watsa labarai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel